23 Satumba 2020 - 10:15
Shugabannin Kasashen Duniya Sun Fara Jawabi A Taron Kolin MDD Karo Na 75

Yau Talata, shugabannin kasashen duniya sun fara jawabi a taron koli na MDD, karo na 75, wanda a bana shugabannin ke jawabi ta kafar bidiyo, sakamakon yanayin da duniya ta fada a ciki saboda annobar cutar korona.

ABNA24 : Shugaba Donald Trump, na Amurka na daga cikin shugabannin da suka gabatar da jawabi.

A cikin jawabin nasa Trump, ya bukaci MDD, data dora alhakin yaduwar cutar korona ga kasar China.

Shi kuwa shugaban China Xe Jenping, zargin Amurkar ya yi da yada kwayar cutar siyasa a MDD.

Shi ma shugaban kasar Turkiyya Reccep Tayib Erdogan, ya yi nasa jawabi inda ya bukaci da a aiwatar da sauye sauye a MDD, musamman a kwamitin tsaro wanda a cewarsa bai kamata ya zama wasu tsiraru ne ba ke juya duniya yadda suke so.

Kafin hakan dai babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteress, ya bukaci duniya ta kaucewa duk abin da zai kawo sabon yakin cacar baki.

342/